Muna goyon bayan gwamnoni kan sulhu —'Yan Shi'a

Wasu 'ya yan mabiya shi'a Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu 'ya yan mabiya shi'a

A Najeriya, kungiyar mabiya akidar Shi'a ta Islamic Movement ta ce ta ce tana goyon bayan yunkurin da kungiyar gwamnonin arewacin kasar ke yi na sasanta rikicin da ya faru tsakanin mabiyanta da sojojin kasar ta hanyar lumana.

Malam Yakubu Yahaya Katsina na daga cikin manyan Almajiran jagoran kungiyar, Sheikh Ibrahim Al ZakZaky, kuma ya shaida wa BBC cewa sun yi na'am da matakin saboda kaucewa zubar da jini.

Ya kara da cewa har yanzu ba su san inda jagoran kungiyar, El-Zakzaky yake ba, yana mai yin kira ga hukumomi da su sake shi cikin gaggawa.

A ranar Juma'ar da ta wuce ne gwamnonin suka jaddada bukatar bin dokar kasa, da yaki da talauci ta yadda za a kaucewa aukuwar rigingimu a nan gaba.

Gwamnonin sun dauki matakin ne bayan rikicin da ya faru tsakanin 'yan Shi'a da sojoji a kwanakin bayan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.