Jam`iyyar PP ta sha kaye a Spaniya

Zaben Spaniya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zaben Spaniya

Mukaddashin Firayim Ministan Spaniya, Mariano Rajoy ya ce zai yi kokarin kafa sabuwar gwamnati, bayan jam'iyyarsa ta Popular Party ta rasa rinjayen da take da shi a Majalisar Dokokin kasar a babban zaben da aka gudanar ranar Lahadi.

Ya yi gargadin cewa akwai bukatar a cimma wata yarjejeniya bayan wasu sabbin jam'iyyun siyasa sun lashe kashi daya bisa uku na kuri'un da aka kada, wato suka kasance kalubale ga jam'iyyun siyasa biyu d suka shafe shekaru gwammai suna cin karensu ba babbaka.

Jam'iyyar Socialist Party dai ita ce ta kasance ta biyu, sai jam'iyyar Podemos wadda ta rufa mata baya, kuma shugabanta Pablo Iglesias ya ce an bude wani sabon babi ne a siyasar Spaniya.

Ya ce, " Yau rana ce ta tarihi a Spaniya. Muna farin cikin cewa an kawo karshen babakeren da jam'iyyun siyasa biyu ke yi, kuma muna murna saboda mun bude sabon babi a siyasar kasarmu".

Ita ma sabuwar jam'iyyar Citizens Party ba a bar ta a baya ba.