Wani harin sama ya hallaka mutane da yawa a Syria

Wani hari a Syria Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga arewa maso yammacin Syria sunce mutane kusan 40 ne aka kashe a wani harin da aka kai da jiragen sama a birnin Idlib da yan tawaye ke rike da shi.

Wurin da aka hara din dai ana jin ceware gine gine ne da kungiyoyin masu kishin Islama da yawa hade da Kungiyar Al-Nusra wadda ake dangantawa da al-Qaida, ke amfani da su.

Mutanen yankin sun ce sun yi amannar jiragen yakin Rasha ne suka kai farmakin, to amma da wuya a tabbatar da hakan.

Haka kuma akwai rahotannin fashewar wani abu a wata motar bas ta soji a Damascus babban birnin kasar.

Gidan Talabijin na Syria ya ce mutane akalla 10 ne suka ji rauni.