'Yan takara jam'iyyar Democrats sun yi muhawara ta karshe

A ranar Asabar ne masu neman tsayawa takarar shugabacin Amurka a tutar jam'iyyar Democrat ke muhawararsu ta karshe a New Hampshire.

Tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hilary Clinton dai ita ce a sahun gaba-gaba, kuma tana karawa ne da Senata Bernie Sanders da gwamnan Maryland, Martin O'Malley.

Mr Sanders ya nemi ahuwar Mrs Clinton dangane da satar bayanai a kan masu zabe da gangaminsa ya yi wa ayarin Hilary Clinton.

Da Mrs Clinton da Mr Sanders duka sun gwabza a kan manufofin gwamnati a kan kasashen waje da yaki da ta'addanci, kana suka tabo al'amuran da suka shafi tattalin arziki a muhawarar.

Sai dai dukkansu, bakinsu ya zo daya wajen caccakar abokin hamayyarsu a jam'iyyar Republican, wato Donald Trump.