'Yan adawa sun yi watsi da rijistar zaben Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Manyan 'yan adawar Nijar

Jam'iyyun adawa a Nijar sun yi watsi da sabuwar rijistar zabe da aka gabatar, sun ce rijistar ta saka ayar tambaya kan sahihancin zaben da ke tafe.

A ranar 12 ga watan Disamba ne, shugaba Mahamadou Issoufou ya amince da bukatar 'yan adawa domin sake tantance rijistar zabe a wani matakin na kokarin samar da zaman lafiya a lokacin zabe.

Sai dai 'yan adawa sun fice daga kwamitin tantance rijistar, abin da ya sa abokan kawancen Shugaba Issoufou ne suka aiwatar da aikin.

Ousseini Salatou, mai magana da yawun jam'iyyun adawa, ya yi watsi da rijistar zaben jim kadan bayan da Firai minista Brigi Rafini ya sanar da kammala aikin tantance rijistar.

Shugaba Issoufou yana neman wa'adin mulki a karo na biyu bayan da ya samu nasara a zaben 2011.