Buhari ya bayar da hakuri kan matsalar fetur

Image caption 'Yan majaliasar dokokin sun sha alwashin yin aiki tare da shugaban kasa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa 'yan kasar hakuri saboda matsananciyar matsalar man fetur din da suke fama da ita.

Shugaba Buhari ya nemi gafara ne a lokacin da yake gabatar da kudurin kasafin kudin shekara ta 2016 a gaban majalisar dokokin kasar.

Shugaban na Najeriya ya ce ya bayar da umarni ga hukumar da ke kayyade farashin man fetur da ta sake duba yadda take kayyade farashin man, yana mai umartar ta da ta tabbatar a yanzu farashin bai wuce N87 kan kowacce lita daya ba.

Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin ne na Naira tiriliyan 6.08 a kan kowacce gangar danyen man fetur $38 da kuma N190 kan kowacce dalar Amurka.

Haka kuma shugaba Buhari ya ce za a ware kashi talatin cikin dari na kasafin kudin domin gudanar da manyan ayyuka, sannan aka ware kashi 70 cikin dari domin yin ayyukan yau-da-kullum.

A bangaren manyan ayyuka, an ware wa ma'aikatar ayyuka da makamashi da kuma gidaje N433.4 bn; yayin da ma'aikatar sufuri ta samu N202.0 bn; inda ayyuka na musamman suka samu N200.0 bn.

An ware N396bn domin bai wa fannin ilimi, yayin da aka ware N296bn kan kiwon lafiya, sannan aka ware N294bn ga fannin samar da tsaro a kasafin ayyukan yau-da-kullum.

Shugaban kasar ta Najeriya ya sha alwashin kwato dukkan kudaden kasar da aka sace, ko da kuwa hakan zai kai shi har karshen wa'adin mulkinsa.