Farashin man fetur na ci gaba da faduwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yanzu ana sayar da gangar danyen mai samfurin Brent a kan $36.

Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya kara samun koma bayan da ba a taba ganin irinsa ba tun shekara ta 2004.

Gangar danyen mai yanzu ta koma kusan dala talatin da shida.

Kasashen da ke amfani da mai na cin ribar wannan faduwar farashi.

Sai dai kasashen da da ke fitar da mai kamar Nigeria, da Venezuela da kuma kasashen yankin Gulf suna fuskantar kalubale ta fuskatar tattalin aziki.