Akwai yaudara a kasafin kudin 2016 — Balarabe Musa

A Najeriya, wasu 'yan adawa a kasar sun ce ba su da karfin gwiwa kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari saboda ba ta dauki hanyar warware matsalolin kasar ba.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, wanda ke mayar da martani game da kudurin kasafin kudi na 2016 da shugaba Buhari ya gabatar wa majalisar dokokin kasar, ya yi zargin cewa akwai yaudara a cikin kasafin.

Alhaji Balarabe Musa ya ce ana yaudarar 'yan Najeriya kawai inda ake ce musu kasa ba ta da kudi, amma kuma ga shi an shirya kasafin kudin da ba a taba yin irin sa a kasar ba.

Ga yadda hirarsu ta kasance da wakilinmu na Kaduna Nura Muhammad Ringim:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti