An zakulo wani da ransa a buraguzai a China

Image caption Inda a ka samu ruftawar kasa a China

An zakulo wani mutun da ransa daga baraguzanan gine-gine bayan sama da sa'o'i 64 da aukuwar bala'in ruftawar kasa da ta janyo rugujewar gidaje a birnin Shenzhen da ke kudancin China.

An gano mutumin ne da asubahin yau Laraba, a wani wurin da ake gina rukunin masana'antu, inda yumbu da dagwalon kwaba suka rufe gine gine da yawa.

Mutumin ya shaida wa masu aikin ceto cewa, akwai wani shi ma da yake da rai a kusa dashi a cikin baraguzan.

Kawo yanzu dai, gawarwakin mutane kadan ne aka gano, sai dai har yanzu ba a ga wasu mutane 70 ba, wadanda ake fargabar sun mutu.