Ana luguden wuta a Ramadi

Image caption Birnin Ramadi nada mahimmanci ga 'yan IS

Jami'an gwamnatin Iraki sun ce dakarun kasar sun kaddamar da hare-hare kan mayakan kungiyar IS.

Wannan wani mataki ne na kokarin karbo tsakiyar birnin Ramadi da ke hannun IS tun a watan Mayun da ya wuce.

Jami'an sun ce sojojin da mayakan sa kai ne ke kai hare-hare ta sama da dakarun hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta na samun nasara tun bayan fara fafatawar a ranar Litinin.

Wakilin BBC ya ce gwamnatin Iraki ta dauki tsahon watanni ta na shirin kai wannan hari, inda ta dauki matakan rufe duk wata hanya da za a iya shiga da kayayyaki birnin, yayin da aka umarci mazauna Ramadin da su bar gidajensu.

An yi kiyasin cewa daruruwan mayakan IS na cikin birnin Ramadi, da ya zama babban gari a yankin Anbar da mayakan Jihadi su ke da karfin fada a ji a wurin.