An mika El-Zakzaky a hannun 'yan sanda

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan shi'a sun ce an kashe 'yan kungiyar da dama

Sufeto Janar na 'yan sandan Nigeria, Solomon Arase, ya ce shugaban kungiyar 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky yana tsare a hannunsu.

Arase -- wanda ya bayyana haka a lokacin da majalisar koli ta addinin musulunci ta ziyarce shi -- ya kara da cewar 'yan uwa da abokan arziki da kuma lauyoyi za su iya ziyartar El-Zakzaky kamar yadda doka ta tanada.

Shugaban 'yan sandan ya kuma jaddada cewar za su ci gaba da aiki domin tabbatar da kare 'yancin dan adam.

Tun da farko, sakataren majalisar kolin, Farfesa Ishaq O. Oloyede ya bukaci shugaban 'yan sanda ya duba abin da ya janyo rikici a Zariya tare da tabbatar da an kauce wa afkuwar hakan a nan gaba.

A ranar 12 ga watan Disamba ne aka samu rikici tsakanin 'yan Shi'a da sojoji a Zariya, lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama.

Tun daga afkuwar rikicin jami'an tsaro suka kama shugaban 'yan Shi'ar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.