Ana ci gaba da gwabza fada a Helmand

Hakkin mallakar hoto MOD
Image caption Dakarun Biritaniya za su kai dauki a yankin

Dakarun gwamnatin Afhanistan na gwabza fada da 'yan bindiga na kungiyar Taliban a wani kokari na sake kwace yankin Sangin da ke lardin Helmand a kudancin kasar.

Jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare biyu ta sama domin taimaka musu.

Gwamnan Helmand, Mirza Khan Rahimi, ya ce sojojin Afghanistan sun sake kwace iko da yankin amma wasu rahotannin sun ce har yanzu ana ci gaba da gumurzu.

Wani kakakin gwamnati ya ce an kashe wani jagoran Taliban din, Mullah Nasir tare da mutanansa su hamsin.