'Yan adawa za su kafa runduna a Burundi

Image caption 'Yan adawa da dama na kurkuku a Burundi

Kungiyoyin 'yan Adawa a Burundi sun sanar da cewa za su kirkiro dakarun hadin gwiwa domin hambarar da shugaba Pierre Nkurunziza daga mukaminsa.

Kungiyar ta kira kan ta Jamhuriyar dakarun kasar Burundi ko Forebu a takaice.

Daruruwan mutane aka kashe a rikicin siyasar da ya barke a kasar, tun a watan Afrilun da ya wuce da shugaba Nkurunziza ya sanar da zai tsaya takarar shugabancin kasar a karo na uku Burundi ke cikin rudani.

Daya daga cikin shugabannin dakarun 'yan tawaye kuma tsohon kanar a kasar, Edouard Nshimirimana ya zargi gwamnatin Burundi da aikata ta'addanci, ya kara da cewa mutanensa za su yi fito na fito domin kare al'ummar kasar da tabbatar da Dimukradiyya.

A ranar litinin gwamnatin Nkurunziza, ta yi watsi da turo dakarun wanzar da zaman lafiya 5000 da kungiyar Tarayyar Afurka ta ce za ta tura kasar.