Sojojin Kamaru sun kashe mutane 70

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamaru na cikin dakarun kawance na murkushe Boko Haram

Dakarun sojin Kamaru sun shiga wani kauyen Nigeria da ke kan iyaka da kasarsu inda suka kashe mutane akalla 70 cikin har da 'yan Boko Haram.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewar dakarun sun shiga kauyen Kirawa-Jimni suna neman 'yan Boko Haram wadanda ke zaune a kauyen.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa, "Akwai 'yan Boko Haram da ke zaune a kauyen, a kullum sai su dinga harbi sama. Rannan nan sai sojojin Kamaru suka zagaye garin, suka ce a nuna 'yan Boko Haram da ke garin, da ba a nuna musu ba, sai suka bude musu wuta."

Bayanai sun ce sojojin Kamaru sun biyo 'yan Boko Haram ne wadanda suka shiga cikin kauyen, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dama.

A cikin watan Nuwamba ma 'yan dakarun Kamaru sun hallaka 'yan Boko Haram kusan 150 a cikin Nigeria sannan suka kona gidaje da dama.