"Kiristanci zai iya bacewa a gabas ta tsakiya"

Image caption Mabiya addinin kirista na bikin kirsimeti a inda suke gudanar da addu'o i a coci - coci a ko ina a duniya

Archbishop na Kantanbury Justin Welby ya yi gargadin cewa saboda hare-haren da kungiyar IS ke kaddamar wa, addinin Kirista ya na fuskantar barazanar bacewa a yankin gabas ta tsakiya inda ya samo asali.

Archbishop Welby zai yi amfani da hudubar da zai gabatar ta Kirsimeti wajen kwatanta kungiyar IS da sarki Herod wanda ya kashe jarirai da yawa a wani yunkuri na kashe Annabi Isa Alaihis Salam da ya samu labarin za a haifa.

A fadar Vatican, Fafaroma Francis ya jagorancin wata addu'ar Mass a jajiberen Kirsimetin, inda ya yi kira ga Kiristoci da su mutunta rayuwa.

A Najeriya da Nijar shugabannin kasar sun yi kira ga mabiya addinan da su zauna lafiya domin karin fahimtar juna da ci gaban kasa.