Yunkurin kwato birnin Ramadi daga IS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaron Iraki na kutsawa layuka domin fatattakar 'yan kungiyar IS a birnin Ramadi.

Jami'an tsaron Iraki na kara kutsawa birnin Ramadi, inda dakarun sojin kasar ke shiga layi-layi suna fafatawa a yunkurinsu na korar 'yan kungiyar IS, wadanda suka kwace iko da birinin tun watan Mayun da ya gabata.

Jami'an tsaro sun ce gwamnati ta kwace ikon yawancin yankunan da ke kusa da tsakiyar Ramadi.

Kakakin gwamnan yankin, Muhannad Haimour ya shaida wa BBC cewa akwai mayakan IS sama da 500 da har yanzu ke garin, kuma yawancin su daga kasashen waje suke, kuma ana kyautata zaton har da 'yan kunar bakin wake cikin su, kuma sun mayar da yara maza da mata fursunonin yaki.

Wani dan majalisar dokokin kasar Mowaffak Al Rubaie ya ce kwato ikon Ramadi daga hannun kungiyar ta IS zai zamo wani babban ci gaba ne da kara kwarin gwiwa ga dakarun Iraki da ke yaki kafada da kafada da 'yan sanda kasar da kuma mayakan Sunni.