Matatar man fetur ta Kaduna ta fara aiki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matatar ta Kaduna ta fara aiki a ranar Laraba a inda ta fitar da lita miliyan 3 na fetur da gas da kuma lita milyan 2 na kananzir

A Najeriya hukumar matatar mai ta Kaduna ta ce ta fara tace danyen mai domin saukake wahalar man da ake fama da ita.

A hirar da BBC ta yi da shugaban matatar Alhaji Sa'idu Mohammed Ali, ya ce a yanzu an shawo kan matsalolin da su ka addabi matatar, ciki har da fasa bututun danyen man da ake turowa daga Warri da ke kudancin kasar.

A cewarsa, a safiyar Laraba sun ba hukumar kula da rarraba man da dangoginsa lita miliyan uku na fetur da gas da kuma miliyan biyu na kananzir.

Sannan ya bayar da tabbacin cewa da zarar an fara dakon mai daga matatar, karancin man da ake fama da shi musamman a arewacin kasar zai ragu.