Ana tuhumar mai shafin Mega-upload

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mai shafin Megaupload, Kim Dotcom

Wata kotu a New Zealand ta yanke hukuncin a mika fitaccen mai hada-hadar intanet din nan, Kim Dotcom ga hannun hukumomin Amurka domin ya fuskanci tuhume-tuhume da ake mu shi na satar fasaha a intanet.

Hukumomi a Amurkan suna zargin shafin Mista Kim Dotcom na intanet, Mega-Upload, da janyo wa wasu kamfanoni asarar dala miliyan 500, saboda ba mutane damar yada fina finai da wakoki da manhajoji da aka saci fasaharsu.

Sai dai Mista Kim Dotcom ya ce bai kamata a tuhumeshi ba, don mutane sun yi amfani da shafin na sa wajen sauke fina-finan ta barauniyar hanya.

Mutumin yana fuskantar daurin shekaru 20 a gidan yari idan an same shi da laifi a Amurka.

Kazalika, kotun ta amince a mika wasu makarraban sa uku da suka yi aiki tare a baya, ga hannun hukumomin Amurkan, sai dai mutanen za su iya daukaka karar.