Cutar Lassa ta kashe mutane biyu a Kano

Image caption Mutanen da suka mutu sun fito ne daga kauyen Dakasoye.

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a jihar sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa.

Jami'in hulda da jama'a na ma'aikakar lafiya ta jihar, Ismaila Garba Gwammaja, ya shaida wa BBC cewa mutanen biyu -- wadanda uba da da ne -- sun fito ne daga kauyen Dakasoye a karamar hukumar Garun-Malam.

Ya ce mutanen sun mutu ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano lokacin da suke karbar magani.

Jami 'in ya ce tuni gwamnatin jihar ta dauki matakan gaggawa na binciken yadda mutanen suka kamu da cutar da kuma hana yaduwar ta.

Har yanzu dai babu bayanin cewa wani ya kara kamuwa da cutar.