Ana neman attajirin Rasha ruwa a jallo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kotun Rasha ta umurci a kamo attajirin nan Mikhail Khodorkovsky.

Wata kotu a Rasha ta bayar da umurnin kamo tsohon attajirin da ke sana'ar harkokin man fetur Mikhail Khodorkovsky, ta kuma ce a sanya shi cikin wadanda duniya ke nema ruwa a jallo.

Ana zargin sa da hannu a kisan da aka yi wa wani magajin gari dan asalin kasar Siberia kusan shekaru 20 da suka wuce.

Mista Khodorkovsky dai na gudun hijira a Turai, amma kuma yana bayar da tallafi ga masu adawa da gwamnatin Rasha, kuma ya ce zargin da ake tuhumar sa da shi na da alaka da siyasa.

Wata mai magana da yawunsa ta ce umurnin da aka bayar na a kamo shi bashi da wani amfani tunda baya kasar.

Khodorkovsky ya shafe shekaru goma a gidan kaso saboda laifin aikata almundahana, amma shekaru biyu da suka gabata shugaba Putin ya yi masa afuwa.