Gobara ta halaka mutane 25 a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AP

Akalla mutane 25 ne suka mutu sannan fiye da 100 suka jikkata a wata gobara da ta tashi a wani asibiti a tashar jirgin ruwa ta Jizan a kasar Saudiya.

Gobarar ta tashi ne da safiyar Alhamis, a hawa na farko na ginin babban asibitin Jizan, wurin da bangaren haihuwa da masu bukatar kulawar gaggawa a asibitin suke.

Ba a gano abin da ya haddasa gobarar ba, amma ana shirin gudanar da bincike.

Jami'an aikin gaggawa sun samu kashe wutar.