'Yar Sri Lanka ta tsallake rijiya da baya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu zanga-zanga a Colombo domin Saudiyya ta janye hukuncin

Gwamnatin Sri Lanka ta ce kasar Saudiyya ta dakatar da hukuncin kisa ta hanyar jefewa, da aka zartarwa wata 'yar Sri Lanka da ke aiki a kasar.

An dai yanke mata hukuncin ne bisa laifin aikata Zina.

Mataimakin Ministan harkokin wajen Sri Lanka, ya ce an dakatar da hukuncin ne bayan kasar sa ta daukaka kara kan hukuncin.

Dayan mutumin da aka yanke musu hukunci tare da shi ma dan kasar ne, an yi masa hukuncin bulala.

Mataimakin Ministan ya ce, za a daure matar da ba a bayyana sunanta ba, a gidan kaso maimakon jefe ta.