An sako karin 'yan Shi'a 83 a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sakin karin mutane 83 da aka kama yayin arangamar da aka yi tsakanin sojoji da 'yan Shi'a a Zariya.

Daga cikin wadanda aka saka akwai mata 49 da kuma maza 34.

Sanarwa daga gwamnatin jihar Kaduna ta ce akwai wasu mutane 191 wadanda ake tuhumarsu da aikata laifukan da suka hada da mallakar makamai da tsare hanya da kuma kai wa jami'an tsaro hari.

Sanarwar ta ce za a ci gaba da tsare wadanda aka kama kafin a gabatar da su a gaban kotu.

Gwamnatin jihar Kaduna din ta kuma bukaci mazauna unguwar Gyellesu da ke Zariya, wadanda suka bar gidajensu sakamakon rikicin, su koma muhallansu saboda an girke jami'an tsaro wadanda za su kare lafiyarsu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ga karin bayani daga Kakakin gwamnan Kaduna, Samuel Aruwan