An haramta yin bikin Kirsimeti a Somalia

Hakkin mallakar hoto Getty

Gwamnatin Somalia ta haramta bikin Kirismeti a Mogadishu babban birnin kasar.

Shugaban ma'aikatar harkokin addini, Sheikh Mohamed Khayrow, ya shaidawa manema labarai cewa yawancin ayyukan bikin kirirsmetin ba su da nasaba da addinin musulinci kuma za su iya tsokano hare-hare daga kungiyar Al-Shabab.

Ya kara da cewa, "An dakatar da duk wani taro na jami'an tsaro, babu wata hidima da za a gudanar."

A shekarar da ta gabata ne dai kungiyar mayakan Al-Shabab suka kai hari wani sansanin sojin kungiyar tarayyar Afrika a birnin Mogadishu, lokacin bikin kirismeti, inda suka hallaka soji biyar.

Yawancin 'yan Somaliya dai musulmai ne.