Cece-kuce kan rijistar zabe a Nijar

Image caption Shugaban Nijar Muhammadou Issoufou na daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar a 2016

Hukumar zabe ta jamhuriyar Nijar CENI, ta yi kira kungiyar kasashen da ke amfani da harshen Faransanci OIF, da ta aiko da kwararru domin binciken rijistar masu zabe da 'yan adawar kasar suka ki amincewa da shi.

Ita dai hukumar CENI ta ce alkawari ta dauka na kwatanta adalci, kamar yadda kundi tsarin mulkin kasar ya yi tanadi.

Bangaren 'yan adawa da hukumar CENI sun yarda cewa akwai kura-kurai da dama a rijistar, amma gwamnati ta kafe cewa ba a bukatar sake dubawa, saboda a cewarsu yin hakan zai iya jawo daga zaben, wanda hakan kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Mataimakin shugaban hukumar zaben Oumarou Khadri, ya shaida wa manema labarai cewa "mun yi rantsuwar yin aiki bisa adalci kuma dole mu cika wannan alkawari."

A watan Fabrairun 2016 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki a Nijar.