Drogba: Montreal na tattaunawa da Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hiddink da Drogba na tattaunawa kan Chelsea

Chelsea na tattaunawa da kungiyar Montreal Impact ta Amurka, a kan batun Didier Drogba.

Kungiyar Montreal inda Drogba ke murza leda ta ce dan kwallon ya nuna sha'awarsa ta "taimakawa tsohuwar kungiyarsa".

"Mun san abin da yake ciki a yanzu, amma manufarmu ita ce ya dawo nan a kakar wasa mai zuwa", in ji Montreal.

Drogba mai shekaru 37, ya koma Montreal ne a watan Yuli, kuma ya kalli wasan da Chelsea ta doke Sunderland tare da kocin riko Guus Hiddink da kuma mai kungiyar Roman Abramovich.

A ranar Laraba, Hiddink ya ki fayyace wa ko Drogba zai yi aiki tare da shi.