Rashin hutu na cutar da Ingila — Klopp

Image caption Klopp na haskakawa a Liverpool

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce yawan murza a gasar Premier ba tare da hutu ba, na janyo wa Ingila nakasu a gasar kasa da kasa.

A cewar Klopp, Ingila na da matasan 'yan kwallon "masu hazaka", amma rashin hutu a lokacin hunturu zai iya hana kasar taka rawar gani a gasar kwallon kasashen Turai a 2016.

"Ana buga wasanni da dama, babu hutu," in ji Klopp.

Dan shekaru 48, Klopp ya ce "Kowa na saran Hodgson ya jagoranci tawagar ta samu nasara."

Ingila ta shafe shekaru masu yawa ba tare da ta kai matsayin zagaren kusa da karshe ba a babbar gasa a duniya.