Turkiyya: Erdogan ya Ceci Wani Magidanci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption shugaban Tirkiyya Tayyip Erdogan

Fadar Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ta ce shugaban kasar ya yi ban-baki ga wani mutumin da ya so kashe kansa bayan ya hau kololuwar wata doguwar gada ya yi barazanar tumowa kasa.

An dai ba da labarin cewa takaici ne ya yi wa mutumin yawa, sakamakon matsalolin iyali, don haka sai ya hau gadar Bosphorous, wadda ta hada Turai da Asiya, ya kuma yi barazanar kashe kansa.

An nuna wasu hotunan Talabijin, inda mukarraban shugaban Turkiyyar ke rarrashin mutumin domin ya saurari shugaban kasar, kuma daga bisani an ciwo-kansa, an kuma sauke shi daga kan gadar.