Boko Haram: Amnesty ta Bukaci Kamaru ta yi Bayani

Hakkin mallakar hoto logo
Image caption Taswirar kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International

Kungiyar kare hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta bukaci mahukunta a kasar Kamaru su yi bayani a kan makomar wasu mutum 130 da aka tsare sakamakon rikicin boko-haram.

Cikin wata sanarwar da ta fitar, kungiyar ta ce an tsare wasu mutane da suka hada da manya da yara 200 a kauyukan Magdeme da Double da ke arewacin kasar, a shekarar da ta wuce.

Amma daga bisani gwamnatin kasar ta ce ta tsare wasu mutum 70 da take zargin cewa 'yan boko-haram ne, sai dai kuma ba ta sake cewa komai a kan sauran mutanen da take tsare da su ba.

A baya dai gwamnatin Kamarun ta musanta zargin da ake mata na azabtarwa da kashe mutanen da take zargin cewa 'yan boko-haram ne ba tare da an musu shara'a ba.