Karin girma sai masu uwa a murhu - Inji 'yansanda a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Sifeto Janar na Nigeria, Solomon Arase

Wasu 'yan sanda a Najeriya sun yi zargin cewa ana yin karin girma a rundunar ne ga wadanda ke da iyayen gida a aikin, maimakon cancanta.

Haka kuma sun yi zargin cewa ana nuna son kai da bangaranci wajen yin karin girman.

Wani jami'in da ya nemi a jirkita muryarsa, ya shaida wa BBC cewa irin wannan nuna wariya, musamman karkashin jagorancin Babban Sifeton 'yan sanda na yanzu, ya fi shafar 'yan sandan da suka fito daga arewacin kasar.

To amma a nata bangaren, rundunar 'yan sandan Najeriya ta musanta wannan zargi.

Kakakin rundunar Mrs Olabisi Kolawole, ta ce lamarin ba haka ya ke ba.