Syria: An kashe madugun 'yan tawaye

Image caption 'Yan tawaye a Syria

Sojin Syria sun ce sun samu nasarar kashe wani madugun 'yan tawaye, Zahra Alloush, bayan wani luguden wuta da suka yi ranar Juma'a.

Sai dai kuma wasu masu kare hakkin dan adam sun ce jiragen yakin Rasha ne suka kaddamar da harin da ya yi sanadiyyar mutuwar jagoran 'yan tawayen.

Alloush dai ya mutu ne tare da wasu manyan kwamandojinsa a lokacin harin da aka kai kan hedikwatarsu da ke a wani yanki na babban birnin kasar, Damascus, wanda kuma yake a arshin ikon 'yan tawayen.

Zahra Alloush da sauran 'yan tawayen da yake jagoranta suna samun goyon bayan Saudiyya, amma kasar Rasha tana yi musu kallo 'yan ta'adda.