Iraq: Sojoji sun fatattaki IS a Ramadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption IS ta fice daga Ramadi

Wasu majiyoyin soji a Iraqi sun ce alamu na nuna cewa mayakan kungiyar masu jihadi ta IS sun fice daga ginin da ke dauke da ofisoshin gwamnati a birnin Ramadi.

'yan kungiyar ta IS dai sun yi garkuwa da wannan gini a lokacin da suke fafatawa da sojojin gwamnati.

Duk da cewa 'yan kungiyar sun fita daga ginin amma akwai fargabar cewa maiyiwuwa ne sun daddasa bama-bamai kafin su fice.

Wakilin BBC ya ce alamu na nuna cewa sojoji na gab da kwato birnin Ramadi wanda ya ke karkashin ikon IS tun a farkon shekarar 2015.