Corsica: An hana zanga zangar kin jinin Larabawa

Wurin Sallar da aka kone a Corsica Hakkin mallakar hoto AFP

Mahukunta a tsibirin Corsica na Faransa sun hana zanga zangar kan tituna a wasu sassa na Ajaccio babban birnin tsibirin sakamakon kwashe kwanaki masu yawa ana zanga zangar kin jinin Larabawa.

Dakarun tsaro a Corsica sun kuma zagaye wani rukunin ginin gidajen da galibi larabawa ne ke zama a cikinsu, inda wasu yan kwana -kwana 2 da dansanda suka samu rauni a wani artabu a ranar 24 ga watan nan na Disamba.

A washe-gari kuma mutane kusan 600 sun hallara domin nunin goyo ga yansanda, daga nan wasu masu zanga zangar suka shiga cikin rukunin gidajen , suka lalata wani wurin sallah.