Guguwa ta kashe mutane 25 a Amurka

Hakkin mallakar hoto Minuteman Disaster Response
Image caption Guguwar ta barke lokacin hutun kirsimeti

Akalla mutane 25 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata mahaukaciyar guguwa da ta barke a kudancin Amurka, a lokacin hutun bukukuwan kirsimeti.

Jihar Texas, ita ce wadda bala'in ya fi shafa a inda guguwar ta yi awon gaba da duk wani abu da ke yankin Dallas, musamman ababan hawa.

Mutane biyar ne suka halaka a unguwar Garland sakamakon taho mu gama da abubuwan da iskar ke dauke da su da mutane.

Har wa yau, guguwar ta kutsa zuwa johohin Mississipi da Tennessee da kuma Arkansas, a inda ta halaka mutane 17.