Yan sandan Brazil na binciken wasu Kurfo

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption brazil police

Rundunar 'yan sandan Brazil na gudanar da bincike ga wasu Kurfo su takwas da ake zargin sun yi wa wasu matasa biyar kwace, bayan sun azabtar da su tare da ci musu zarafi lokacin da ake bukukuwan Kirsimati.

Matasan sun ce 'yan sandan Kurfon sun tsare su ranar Juma'a da daddare, lokacin da suke komawa gida a kan babura, bayan sun sha ruguntsumi ko dabdalar Kirsimati.

Sun kara da cewa 'yan sandan suna cike da takaicin cewa an saka su aiki ne a ranar bikin Kirsimeti, don haka sai suka huce fushinsu ne a kan su.

Wakilin BBC ya ce wannan zargin kwace da cin zarafin jama'a da ake yi wa 'yan sanda zai iya baro-liki, ganin cewa saura wata shida a yi gasar wasannin motsa-jiki a birnin Rio, inda dubban 'yan wasa daga sassan duniya za su taru.