Taro domin kawo karshen rikicin Burundi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tazarcen shugaba Nkurunziza ne ya janyo rikici

Wakilai daga bangaren gwamnatin Burundi da na 'yan adawa da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma na coci-coci suna taro a Uganda, domin tattaunawa kan yadda za a kawo karshen rikicin siyasar da yaki-ci-yaki cinyewa a kasar.

Shugaba Pierre Nkurunziza, wanda matakin da ya dauka na takarar shugaban kasa a karo na uku ita ta haddasa barkewar tashin hankali, bai halarci zaman bude taron na yini guda ba.

Kungiyar kasashen Afrika ta gabas dai ta dora wa shugaban Uganda, Yoweri Museveni alhakin yin sulhu kan rikicin.

Tuni kungiyar Tarayyar Afrika ta sanar da cewa za ta aika dakaru 5,000 domin wanzar da zaman lafiya a Burundi.