Boko Haram na boye a tsaunukan Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Boko Haram

Yayin da Sojojin Najeriya ke ikirarin karya-lagon kungiyar Boko Haram, an yi amanna cewa mayakan kungiyar da dama suna nan boye a tsaunukan da ke iyakar Najeriyar da kasar Kamaru.

Wasu daga cikin mayakan kungiyar na ketarawa kasar ta Kamaru, inda ake kai hare-hare da dama, kuma akalla mutum 400 ne aka kashe a arewacin kasar.

'Yan mata ne dai ke kai hare- hare irin na kunar bakin wake a kasar ta Kamaru.

A baya-bayanan 'yan mata sun kai hare- hare irin na kunar bakin wake sau 7, wanda daya daga cikin hare- haren ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 a wata kasuwa.