An kashe mutane 50 a Maiduguri da Adamawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane akalla dubu 17

Akalla mutane 50 ne suka mutu sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram a jihohin Adamawa da kuma Borno a arewa maso gabashin Nigeria.

Wadannan hare-hare sun auku ne tun daga ranakun Lahadi zuwa Litinin.

A harin da 'yan Boko Haram din suka kai kasuwar Madagali ranar Litinin, wani dan kasuwar ya shaida wa BBC cewa bam daya ya tashi ne a mahautar kasuwar, yayin da dayan ya tashi a wurin da ake sayar da hatsi.

Ya kuma ce ya ga gawarwakin mutane sama da ashirin da biyar.

Tuni dai hukumomi a jihar suka bada sanarwar rufe kasuwar.

A jihar Borno ma akalla mutane 20 ne suka mutu ranar Litinin da safe bayan da wata 'yar kunar bakin wake ta ta tashi wani bam dinda ke jikinta a kusa da wani masallaci a Maiduguri.

Mutane da dama ne dai yanzu haka suke kwance a asibitoci daban daban a jihohin biyu sakamakon wadannan hare-hare.

Wadannan hare- hare na zuwa ne bayan Sojojin Najeriyar sun yi ikirarin karya-lagon kungiyar Boko Haram.

Wasu bayanai sun ce mayakan Boko Haram da dama suna nan boye a tsaunukan da ke iyakar Najeriyar da kasar Kamaru.

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya bai wa sojojin Kasar wa'adi zuwa karshen shekara da su murkushe 'ya'yan kungiyar Boko Haram.