An kashe akalla mutane 20 a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption Mayakan Boko Haram na ci gaba da kai hare hare

Akalla mutane 20 ne suka mutu bayan wata 'yar kunar bakin wake ta tayar da bam dinda ke jikinta a kusa da wani masallaci a unguwar Ushari Bulabulin a Maiduguri ranar Litinin da safe.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa BBC cewa 'yar kunar bakin waken ta tayar da bam din ne a lokacin da ta kutsa kai inda ake binciken mutane wanda ke kusa da masallacin.

Mutane kimanin shida zuwa bakwai ne kuma suka jikkata a lokacin da bam din ya fashe in ji mazaunin unguwar.

Sai dai hukumomin soji ba su ce komai game da wannan sabon harin na baya-bayan nan ba.

Wannan hari dai na zuwa ne kasa da sa'oi 24 bayan da sojojin suka ce sun dakile wani hari a Maiduguri, babban birnin jihar Borno

Hukumar bada agajin gaggawa a Najeriyar shiyyar arewa maso gabas ta ce mutane 21 ne suka mutu, wadansu 91 kuma suka jikkata a harin na ranar Lahadi da yamma.