An dakatar da tantance `yan sanda a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Babban Sifetan `yan sandan Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya da kuma hukumar 'yan sandan kasar sun ce an dakatar da shirin tantance jami'an 'yan sanda da ke da shaidar kammala digiri ko kuma babbar diploma yayinda suke aiki da nufin yi musu karin girma.

Matakin ya biyo bayan zargin da ake yi cewa akwai masu takardun shaidar kammala karatun na jabu daga cikin jami'an 'yan sandan.

Hukumomin sun ce za a yi amfani da masu bincike masu-zaman-kansu don tabbatar da sahihancin shirin tantancewar.

Ana sa ran bayan kammala tantance 'yan sandan, kowace jiha za ta samu kaso daidai da sauran jihohin Najeriya, na adadin 'yan sandan da za a yi wa karin girma.