Wagegen giɓi a kasafin kudin Saudiyya

Image caption Sarki Salmanu na Saudiyya

Kasar Saudiyya ta sanar da samun gibi har na dala 98 a kasafin kudinta na shekarar 2015, sakamakon faduwa warwas da farashin mai ya yi a kasuwar duniya.

Ta kuma yi hasashen samun wani gibin har na dalar Amurka 87 a kasafin kudin kasar na sabuwar shekara mai kamawa, wanda shi ne gibi na uku da kasafin kasar ya ke, cikin shekaru uku a jere.

Ma'aikatar kudi Saudiyyar, ta ce za ta sake yin duba ga tallafin da ake bai wa sha'anin lantarki da na man fetur din, sannan kuma a sayar da wasu sassan gwamnati ga masu zuba jari.

Sai dai kuma masu sharhi kan al'amura na yi wa kallon irin kudaden da Saudiyyar take kashewa a yakin da take yi da 'yan Shi'a a Yemen, a matsayin makasudun samun gibin da kasar take samu a kasafin kudaden nata.