An haramta yi wa mata kaciya a Gambia

Majalisar dokokin Gambia ta amince da wani kudurin doka na haramta yi wa mata kaciya.

Majalisar dokokin ta kada kuri'a da gagarumin rinjaye na haramta yiwa mata kaciyar a ranar Litinin, wata guda bayan da Shugaban Kasar Yahya Jammeh ya bayyana matakin da cewa ya saba musulunci.

Karkashin sabuwar dokar, wadanda aka samu suna yin kaciyar za su fuskanci daurin shekaru uku da kuma tarar dala dubu daya da dari uku ko kuma duka.

Majalisar dinkin duniya ta ce an yiwa kashi uku bisa hudu na al'ummar mata a kasar kaciya.