An kashe jagororin IS 10 a Syria

Hakkin mallakar hoto AP

Rundunar sojin Amurka tace hare- haren saman da kawancen sojojin dake yakar mayakan IS ke kai wa a Syria da kuma Iraqi ya yi sanadiyyar hallaka jagororin mayakan IS su 10 a cikin wata daya gabata.

Wadanda aka kashe sun kuma hada da daidaikun mutanen da ke da alaka da hare- haren da aka kai birnin Paris a watan Nuwamba.

Wani mai magana da yawun gamayyar sojojin da Amurka ke jagoranta Kanal Steve Warren ya ce daya daga cikin mutanen da suka mutu shi ne Charaffe al Mouadan- wani mamban kungiyar dake a Syria, wanda kuma ke da alaka ta kai tsaye da wanda ya jagoranci hare- haren da aka kai birnin Paris