An hallaka 'yan jarida 69 a 2015

Image caption 'Yan jarida na fuskantar hadari a wajen gudanar da aikinsu

An samu karuwar mutuwar 'yan jarida a bakin aikinsu, a wannan shekara mai karewa ta 2015.

Kungiyar da ke kare hakkin 'yan jarida ta duniya ta ce 'yan jarida 69 aka kashe a wannan shekara, kuma wannan adadi ya zarta na bara da mutum takwas.

Kungiyar ta ce kungiyoyi irin su IS da Alka'ida su ne suka kashe kashi 40 bisa dari na wannan adadi, kuma kasar Syria ce mafi hadari ga aikin jarida.

Binciken dai ya ce dadadin 'yan jaridar da ake kashewa yana iya zarta wadannan alkaluma da aka fitar, saboda akan fuskanci matsala wajen gudanar da wani binciken.