Mu na da kyawawan manufofi ga Nigeria—Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buharin ya ce gwamnati na da shirin sasantawa da kungiyar Boko Haram domin sako 'yan matan makarantar Chibok sama da 200 da aka yi garkuwa da su a bara.

Shugaba Buhari wanda ya sanar da hakan a tattaunawa ta musanman da 'yan jarida, 'Presidential Media Chat' karo na farko tun bayan da a ka rantsar da shi, ya ce gwamnati ta na jiran ta samu jagororin kungiyar na gaskiya.

Ya ce gwamnati ta na so ta samu jagororin kungiyar Boko Haram da za su bayar da tabbaci game da inda 'yan matan na Chibok suke, sannan ta fara tattaunawa da su.

A game da arangamar sojoji da 'yan Shi'a a Zaria kuwa, shugaba Buhari ya ce ba zai ce komai ba a matsayinsa na Shugaban kasa, sai ya samu rahoton bincike kan lamarin, sannan zai sanar da matakin da za a dauka.

Sai dai duk da haka, shugaba Buhari ya ce bai kamata wata kungiya ta rika karya doka ba, sannan ta zamo tamkar gwamnati mai zaman kanta, a cikin wata kasa mai cikakken 'yan ci.

Dangane da yaki da cin hanci da rashawa kuwa, shugaba Buhari ya musanta zargin da ake mushi cewa ya fi karkatar da yaki da cin hanci da rashawa ga 'yan adawa.

Shugaban ya ce ba gaskiya ba ne da ake cewa ya na kawar da kai daga 'yan jam'iyyarsa wadanda a ke zargi da wawure dukiyar kasa, inda ya ce duk wani mai shaida dake nuna wani daga cikin ministocinsa ba shi da gaskiya to ya gabatar da ita.

Ya sha alwashin sauke duk ministansa da aka tabbatar ya yi kwanciyar mugirbi akan dukiyar kasa, tare da hannunta shi gaban kuliya.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa na da kyawawan manufofi ga Najeriya.