Kokarin ceto mahakan da suka makale a China

Hakkin mallakar hoto Xinhua
Image caption Inda aka samu hadarin

Masu aikin ceto a China na ta fafutukar kai wa ga wasu mahaka ma'adinai su takwas da suka makale a karkashin kasa bayan da wata mahakar ma'adinai ta rufta a lardin Shandong ranar Juma'ar da ta gabata.

Zuwa yanzu dai masu ceton sun tura wa mahakan abinci da fitilu ta cikin wasu ramuka, amma fadowar duwatsu da kuma kwararar ruwa ba zato-ba-tsammani na yi wa aikin ceton cikas.

Wakilin BBC ya ce ba a san irin raunin da mahakan suka yi ba, balle makomar abokan aikinsu wadanda suka makale a lokaci guda.

Mahaka tara ne ba a san halin da suke ciki ba, yayin da daya ya riga mu gidan gaskiya.

Shi ma mai mahakar ya kashe kansa a karshen mako.