Nigeria ta rage kwabo 50 a farashin mai

Image caption 'Yan bumburutu na cin kasuwa idan ana fama da karancin mai a Nigeria

Gwamnatin Nigeria ta ce daga ranar daya ga watan Janairun, 2016, duka gidajen mai mallakar kamfanin NNPC za su koma sayar da man fetur a kan naira 86 kowace lita.

Shugaban hukumar kayyade farashin man fetur a kasar - PPPRA, Farouk Ahmed wanda ya bayyana haka, ya kara da cewa gidajen mai na 'yan kasuwa za su dinga sayar da man a kan naira 86 da kwabo 50 a kan kowace lita.

A cewarsa, an rage farashin man fetur din ne bayan da aka sake lissafi a kan farashin da ya kamata a sayar da man fetur da kuma kalanzir.

Ahmed ya kara da cewa idan har ba a samu sauyi ba, wannan farashin ne zai kasance har zuwa watan Maris na 2016.

Shugaban na PPPRA, ya ce duk dan kasuwar da aka samu yana sayar da man fetur fiye da kayyadajjen farashi na gwamnati, zai fuskanci fushin hukuma.