Mai yiwuwa a hana sanya hijabi a Nigeria

Image caption 'Yan matan Chibok

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce mai yiwuwa gwamnatinsa ta haramta sanya hijabi idan 'yan Boko Haram suka ci gaba da yin amfani da mata domin kai hare-haren kunar bakin-wake a kasar.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi ga rukunin 'yan jaridu ta gidan talbijin din kasar ranar Laraba da daddare.

Wani dan jarida ne dai ya tambayi shugaban kan cewa ko idan hare-haren kunar bakin-wake suka ci gaba za a iya haramta sanya hijabi kamar yadda wasu kasashe suka hana sanya nikabi ko burqa, sai Buhari ya ce "Kwarai hakan ka iya faruwa".

Hijabi dai ya kasance suturar matan aure da 'yan mata Musulmi masu daman gaske a Najeriya, musamman ma a arewacin kasar.

Sai dai a baya-bayan nan hare-haren kunar bakin-wake da 'yan mata masu sanye da hijabin ke yi sun fara sanya shakku a zukatan mutane dangane da kimar macen da take sanye da irin wannan tufafi.

Sauran batutuwan da shugaba Buharin ya yi tsokaci kai yayin hirar sun hada da kisan da aka yi wa mabiya mazhabin Shi'a da rikicin Biafra da rashawa da cin hanci da kuma batun hana yin amfani da katin ATM wajen cire kudade a kasashen waje.