An kara farashin man fetur a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saudiyya tana da gibin $ 98bn a kasafin kudin kasar na wannan shekarar sakamakon faduwar farashin fetur.

Farashin man fetur ya karu da kusan rabi a Saudi Arabia, a alamun farko na matakan tsuke bakin aljihun da gwamnatin kasar ke dauka da nufin cike gibin da faduwar farashin danyen man fetur ta haifar.

An samu hauhawar farashin ne bayan da gwamanti ta ba da sanarwar janye tallafin da take bayarwa ga wasu abubuwan bukatu na yau da kullum a kasafin kudinta na badi.

Har yanzu dai farashin man na da matukar sauki a Saudi Arabia idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya.

Ranar Litinin kasar ta Saudi Arabia ta ba da sanarwar gibin da ba a taba samun irinsa ba, na dala biliyan 98 a kasasfin kudi na bana.