"Kasashen Turai sun gaza kan 'yan hijira"

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mista Antonio Guterres

Babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya mai barin gado ya yi kakkausan suka kan matakin da kasashen Turai ke dauka game da 'yan gudun hijira.

Antonio Guterres -- wanda yake shirin barin aikinsa bayan ya shafe shekaru 10 a hukumar kula da 'yan gudun hijiran ta majaliasar -- ya shaida wa BBC cewa Tarayyar Turai ba ta cikin shiri lokacin da 'yan gudun hijira daga Syria suka fara kwarara Turai.

Ya ce a karon farko 'yan gudun hijira masu yawan gaske sun yi ta kwarara nahiyar Turai, kuma har yanzu kasashen Turai ba su shirya karbar 'yan gudun hijirar ba.

Mista Guterres ya ce rabuwar kai a tsakanin kasashen Turan ta hana su daukar mataki na bai-daya, inda har ma wasu kasashen Turan suka tsaya kai-da-fata domin ganin 'yan gudun hijiran sun fice daga cikinsu.

Ya ce a halin yanzu kimanin mutane miliyan 60 ne suka rasa matsugunansu a fadin duniya, idan aka kwatanta da mutane miliyan 38 da aka samu bara.